Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babu Matsiyacin Da Zai Hana Mu Shiga Siyasa -Ɗan El-Rufai Ga Al'umma

Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; Bashir El-Rufai da ga Gwamnan jihar Kaduna, kuma kani ga Bello El-Rufai wanda ya ci zaben fidd...


Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; Bashir El-Rufai da ga Gwamnan jihar Kaduna, kuma kani ga Bello El-Rufai wanda ya ci zaben fidda gwani domin tsayawa takarar majalisar Tarayya mai wakiltar Kaduna ta Arewa, ya ce babu matsiyacin da ya isa ya hana su shiga siyasa. 

Bashir El-Rufai ya wallafa hakan ne a shafinsa na Facebook. Inda ya ce; "Mu 'yan Nigeria ne kuma babu wani matsiyaci da zai hana mu shiga siyasa dan mun taso a chikin gata ko Mahaifin mu ne gwamna da ya ma kusa barin offishi ya huta. Ba zabin mu ba ne. Allah ne", inji shi.

Ya kara da cewa; "Idan hassadan ka kenan toh kasan da Allah ka ke fushi. Siyasan nan sai mun yi ta. Kuma Sai mun samo nasara kuma ba Dan Adam da ya isa hana mu sai Allah Ubangiji", ya jaddada. 


Jaridar MADOGARA ta lura da yadda masu bibiyarsa suka rika caccakarsa da nuna masa cewa sam ba shi da 'tarbiyya'. 

      Bashir da Bello El-Rufai, 'ya'ya ga Nasiru El-Rufai

No comments