*Hukuma ce ke da hurumin yanke hukunci ga wanda ya zagi Annabi, ba ‘dai’daikun mutane ba. *Ya kuma yi kira ga Hukumomi da su dinga zarta...
*Hukuma ce ke da hurumin yanke hukunci ga wanda ya
zagi Annabi, ba ‘dai’daikun mutane ba.
*Ya kuma yi kira ga Hukumomi da su dinga zartar da
hukuncin kisa ga wanda ya zagi Annabi (S) Kafin jama’a su kai ga nasu hukuncin,
Wannan ne kadai zai hana’dai’daikun mutane daukar mataki na kisa.
Kungiyar wa’azin musulunci ta Izalatil Bidi’ah wa
iqamatis sunnah a tarayyar Naijeriya tayi Allah wadai da wata yarinya wacce ba
musulma ba da ta zagi Annabi Muhammadu tsira da aminci su kara tabbata a gare
shi . Yarinyar mai suna Debora wacce ke karatu a kwalejin Ilimi dake jihar
sokoto, tayi mummunan zagi a wani zaure na WhatsApp da suka bude a matsayin su
na dalibai domin tattaunawa, Yarinyar ta kunduma ashariya ga Annabi (SAW) wanda
duk musulmi bazaiji dadi ba, wanda hakan har yakai ga wasu jama’a suka kasheta
kuma suka kona ta. Addinin musulunci bai bada dama ga musulmi ya zagi ko wane
Annabi daga Annabawan Allah ba, dan haka akwai bukatar shugabannin kiristoci su
dauki aniyar wayar da kan mabiyansu akan illar taba mutunci ko zagin fiyayyen
halitta wanda hakan ka iya tayar da husuma a cikin kasa.
Sheikh Bala Lau yayi kira na musamman ga hukuma da
ta dinga saurin daukan mataki na kisa ga wanda ya zagi Annabi (S) da wannan shi
zai hana jama’a daukar nasu matakin, amma jama’a suna ganin ko an damka wanda
yayi zagin ga hukuma Masu kare hakkin dan Adam zasu shigo ayi ta bugawa wanda
hakan zai sa a saki wanda yayi zagin, yaci gaba da rayuwar sa ba tare da daukan
matakin na shari’a a kansa ba. “Dan haka Ina kira ga hukumomi da su dinga
aiwatar da hukuncin kisa ga wanda yayi zagin, Wannan ne kadai zai gamsar da
mutane su daina daukar doka a gannunsu” Inji Shi.
Shugaban IZALA Sheikh Bala Lau ya kuma yi kira ga
jama’a a duk lokacin da irin haka ya faru idan an kama wanda yayi zagin babu
wani wanda yake da hakkin zartar wa wani haddi ko hukunci akan tuhumar da ake
masa, har sai an gabatar da shi gaban alkali, shi ne wanda zai iya tabbatar
masa da wannan laifin ko ya wanke shi.
“Al-Imam An-Nawawi: “Babu wanda yake da hurumin
tsayarwa da mutane masu ‘yanci haddi sai shugaba, ko wanda shugaba ya nada,
domin babu wanda ya taba zartar da hukuncin haddi akan wani a zamanin manzon
Allah (S.A.W) sai da izininsa. Haka abin yake a zamanin halifofinsa duka.
Saboda tsayar da haddi wani abu ne da yake bukatar zuzzurfan ilimi, kuma za a
iya yin zalunci a cikinsa, don haka bai halatta ba sai da izinin shugaba”.
[Al-Maj’mu’, juz’i na 20, shafi na 34].
Al-Imam Al-Kurtubi: “Babu sabani tsakanin malamai
cewa, haddin kisa, babu wanda yake da hurumin tsayar da shi sai shugabanni. Su
ne aka dora musu wannan alhaki a wuyansu”. [Tafsirinsa, Bakara, aya ta 187].�A wani gurin
yana cewa, “Malaman fatwa sun yi ittifaki kan cewa, ba ya halatta ga wani ya yi
wa wani haddin kisa, in banda shugaba. Mutane a junansu ba su da wannan hakkin.
Wannan hakkin shugaba ne ko wanda shugaba ya nada”. Tafsirinsa, Bakara, aya ta
179.
Malam Ibn Rushd: “Malamai sun yi ittafiki cewa,
shugaba ne kadai yake da hakkin tsayar da haddi” Bidayatul Mujtahid, juz’i na
4, shafi na228.
Don haka dole ne jama’a su fahimci, kuma su fahimtar
da cewa, wannan aiki da wasu suka dauka ba koyarwar musulunci ba ne, kuma ba
wani malami na musulunci da ya taba fatawar aikata irin wannan aika-aika da
sunan son Annabi (S.A.W), ko kishin musulucni, kuma musulunci yana tir da irin
wannan ta’asa a duk inda aka yi ta.
A karshe shehin Malamin yayi kira ga hukumomi Kira
ga hukumomi da kan daukan mataki domin hukunta masu irin wannan laifi da
gaggawa don toshe kafar hana irin wannan saboda masu daukan doka a hanu.
No comments