Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bayan Shekara 11 AC Milan Na Daf Da Lashe Kofin Serie A

  Sandro Tonali ya kai AC Milan kusa da lashe gasar Serie A ta kasar Italiya da kwallaye 2 da ya ci musu a wasa tsakaninsu da Verona  a jiya...

 


Sandro Tonali ya kai AC Milan kusa da lashe gasar Serie A ta kasar Italiya da kwallaye 2 da ya ci musu a wasa tsakaninsu da Verona  a jiya Lahadi, abin da ya sa suka ci gaba da bai wa Inter Milan tazarar maki 2 a saman teburin gasar ta Italiya.

Dan wasan tsakiyar na Italiya ya ci kwallaye 2 masu kamanceceniya da juna san nan Alessandro Florenzi ya karasa aikin a kusan karshen wasan, lamarin da ya sa yanzu AC Milan din ke bukatar maki 4 kacal daga wasanninsu 2 da suka rage don lashe kofin Serie A din su na farko tun bayan shekarar 2011.

Rawar gaban hantsi da suka yi a wasanni hamayya 2 da suka fafata da Inter Milan zai sanya masu rike da kofunan zakarun nahiyar Turai har 7 a gaba idan har suka yi kankankan a yawan maki karshen kaka.

Kocin AC Milan Stefano Sampaoli ya bayyana jin dadinsa a game da wannan nasara, yana mai bayyana irin soyayyar da yake yi wa ‘yan wasansa.

Milan za ta fafata da Atlanta da ke neman zuwa gasar Turai a karshen mako mai zuwa kafin daga bisani su yi balguro zuwa Sassuolo a mako karshe na gasar Serie A.

No comments