Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Benzema Ya Cimma Yawan Kwallayen Da Raul Ya Ci A Real Madrid

Karim Benzema ya cimma Raul Gonzales a matsayin dan wasa na 2 mafi yawan kwallaye a Real Madrid, a yayin da Vinicius Junior ya ci kwalaye 3 ...Karim Benzema ya cimma Raul Gonzales a matsayin dan wasa na 2 mafi yawan kwallaye a Real Madrid, a yayin da Vinicius Junior ya ci kwalaye 3 rigis a fafatawar da suka lallasa Levente 6-0.

Benzema mai shekaru 34 ya ci wata kwallo da ka, lamarin da ya sa yanzu kwallayensa daidai da Raul, wato 323, Cristiano Ronaldo ne kawai ya ci wa kungiyar kwallaye 450.

Sakamakon wannan wasa, yanzu Levente ta rikito daga gasar La Ligar Spain, inda yanzu ta koma rukunin ‘yan dagaji.

Gabanin wasan, Levante  na bukatar samun nasara Santiago Bernabeu, haka ma a sauran wasanninta 2 na karshen kaka, amma hakan bai samu ba ganin yadda ta fadi warwas a wasa tsakaninta da Real Madrid.

Real Madrid, a karkashin jagorancin Carlo Ancelotti za ta yi karon batta da Liverpool a wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Turai da za a fafata  a ranar 28 ga watan Mayu a birnin Paris na Faransa.

No comments