Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bikin Sallah: Saraki Ya Nemi Musulmi Su Yi Addu’ar Zaman Lafiya

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya mika sakon taya murna ga al’ummar musulmin Nijeriya b...Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya mika sakon taya murna ga al’ummar musulmin Nijeriya bisa kammala azumin Ramadana na wannan shekara, tare da murnar bikin sallah karama.

Saraki a wata sanarwar manema labarai wanda shugaban sashen watsa labarai na ofishinsa, Alhaji Yusuph Olaniyonu ya fitar ya shawarci ‘yan Nijeriya da su kara kaimi wurin yin addu’o’i don bunkasar Nijeriya.
Ya kara da cewa Ramadan lokaci ne da Allah ya hore mu da nuna kauna ga juna da kuma yin rayuwa mai nagarta ta hanyar kauracewa munanan dabi’u.

“Kamar yadda gabadayanmu aka hore mu da kauracewa duk wasu munanan dabi’u a lokacin azumin Ramadana, ya kamata a ce ba kawai a wannan wata ba, a gabadaya rayuwarmu haka za mu rika tafiyar da ita.” Inji shi. 

Haka nan kuma, Saraki ya yi addu’ar Allah Ya yi wa ‘yan Nijeriya jagoranci wurin zaben shugabanni managarta a yayin da babban zaben shekarar 2023 ke karatowa. “Allah Ya sa mu zabi mutanen kirki wadanda za su ceto Nijeriya daga halin da take ciki”.

No comments