Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Buhari Na Kwana Da Talakan Nijeriya A Ransa, Inji Gwamna Badaru

  Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ya damu da halin da kasar ke ciki, ta inda a kullum talaka ne ...

 


Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ya damu da halin da kasar ke ciki, ta inda a kullum talaka ne a ransa.

Badaru, wanda shi ne shugaban zabukan fid da gwani na gwamnoni a jam’iyyar APC mai mulkin kasar ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi a wani shirin siyasa ta wata tashar talibijin a  kasar.

Badaru ya ce da tsoron Allah Buhari yake gudanar da gwamnatinsa, tare da iya kwarewar da yake da ita, hasali ma da tunanin yadda zai kyautata rayuwar talakan kasar yake kwana.

Gwamnan ya ce jam’iyyar APC ta gaji matacciyar kasa ne daga hannun PDP, kuma ta dage har sai da ta tabbatar ta farfado da ita, yana mai cewa ‘yan Najeriya suna sane da abin da PDP ta yi kuma ba za su taba zabenta ba.

Ya kara da cewa ba a manta da ta’asar da aka yi daga shekarar 1999 zuwa yanzu ba, saboda haka APC za a yi  a zabe mai zuwa.

No comments