Buhari Ya Ba Da Umarnin Gurfanar Da Mutanen Da Suka Fille Kan Sojoji

 


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya kadu matuka da samun labarin harbe wani jami'in soja da wata abokiyar zamansa sannan aka fille musu kai a yankin kudu maso gabashin kasar.

Shugaban ya ba da umarnin a gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kotu.

Hukumomin kasar sun zargi kungiyar ‘yan aware ta Biafra da kashe ma’auratan a lokacin da suke tafiya daurin aurensu a karshen makon jiya.

Kungiyar dai ta musanta hannu a kisan.

'Yan bindiga a kudu maso gabashin Najeriya a 'yan kwanakin nan sun zafafa kai hare-hare kan jami'an tsaro.

Post a Comment

0 Comments