Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Buhari Ya Ja Kunnen Sojoji Bayan 'Yan Bindiga Sun Kashe Da Dama A Zamfara

  Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gargadi hukumomin sojin kasar  cewa kada su yi kasa a gwiwa wajen yakin da suke da ayyukan ‘yan bindiga...

 


Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gargadi hukumomin sojin kasar  cewa kada su yi kasa a gwiwa wajen yakin da suke da ayyukan ‘yan bindiga, a yayin da yake mayar da martini ga kisan dimbim mutane da ‘yan bindiga suka yi a karshen mako.

Ya ce wajibi ne sojojin su tabatar da cewa ba a koma irin lokacin da ‘yan bindigar ke cin karensu babu babbaka ba, duba da irin mawuyacin hali da al’umma suka shiga.

Shugaban ya yi wannan gargadi ne a wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar, biyo bayan hare haren da ‘yan bindiga suka kai kauyukan Sabon Garin Damri da Kalahe a karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfara, inda tsakanin mutane 40 zuwa 56 suka mutu.

Mazauna yankunan sun ce ‘yan bindigar sun shiga Sabon Garin Damri a ranar Juma’a bisa Babura, inda suke ta harbi kan mai uwa da wabi, tare da kai hare hare a kan wani asibiti.

Makonni 2 da suka wuce, fiye da ‘yan bindiga  10 ne dakarun Najeriya suka kashe a karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfarar bayan wata arangama, inda suka karbe dimbim dabbobi da  ‘yan bindigar suka sace.

Bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa sojojin kasar saboda jajircewarsu, ya bayyana cewa har yanzu da sauran rina a kaba a game da  masu aikata laifukan ta’addanci, saboda haka dole dakarun kasar su ci gaba da rike wuta don kakabe mugaye gaba daya.

No comments