Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bukatar Da IPOB Ta Bijirowa Da Buhari A Yayin Ziyararsa Jihar Ebonyi

  Kungiyar IPOB da ke fafutukar kafa kasar Biyafara daga Nijeriya, ta bukaci shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, da ya gaggauta sakin Nnamdi...

 


Kungiyar IPOB da ke fafutukar kafa kasar Biyafara daga Nijeriya, ta bukaci shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, da ya gaggauta sakin Nnamdi Kanu jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB.

IPOB ta yi wannan kira ne, a yayin da Buhari ke shirin fara ziyarar yini biyu a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin kasar daga yau Alhamis.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, shugaban kungiyar MASSOB Uchenna Madu ya kuma bukaci da a bai wa dan kabilar Igbo damar kasancewa shugaban Nijeriya a zaben shekara mai zuwa ta 2023, baya ga sakin Nnamdi Kanu.

An dai kama Kanu ne tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin aikata laifukan ta’addanci da cin amanar kasa, zarge-zargen da ya musanta.

Bayan kafuwar kungiyar IPOB da kotu ta haramta, mayakanta sun sha kai hare-hare a kan hukumomin tsaro da cibiyoyin gwamnati da manyan mutane bayan kama jagoransu Mista Kanu Nnamdi Kanu da jami’an tsaro suka yi. Sai dai kungiyar ta sha musanta cewa ba su ne ke kai hare-haren ba. 

Yayin da yake tsokaci kan halin da ake ciki, shugaban masu fafutukar na kungiyar MASSOB wato Madu, ya ce ba sa adawa da ziyarar da shugaban kasa a yankinsu na kudu maso gabashin Turai, sai dai ya nanata cewar sakin mista Kanu zai kwantar da hankula a yankin.

No comments