Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bukin Karrama Kwamandar Police Neighborhood Watch Shiyyar Tafa Ya Yi Armashi

Daga A'isha Suleman Zariya Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun karrama shugaban rundunar Police Neighborhood W...


Daga A'isha Suleman Zariya

Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun karrama shugaban rundunar Police Neighborhood Watch dake garin Tafa a karamar hukumar Kagarko na jihar Kaduna.

Bikin an gudanar da shi ne a babban dakin taro na Alhaji Ibrahim Musa Dan kwairo dake garin Tafa.

Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka halarci wannan taro.

Bayan dakin taro ya cika ya batse ne kuma dukkan manyan baki sun iso sai aka bude taro da addu'a kamar yadda aka saba a wajen taro.

Fitaccen Dan wasan kwaikwayon nan na Kanyywood wato Sinana shi ne MC a wannan taro.

Farfesa Buhari Isa shi ne ya wakilci kungiyoyin da suka bayar da lambar yabon.

Kadan daga cikin gamaiyar kungiyoyin da suka karrama kwamandan rundunar sun hada da National Human Rights Ambassadors Organizations da International Peace Committee For Interfatth Harmony da wasu guda 10 da suke da rassa a kasashen duniya da nan gida Nijeriya.

Wakilin kungiyoyin Farfesa Buhari a yayin da yake jawabi akan dalilinsu na karrama Kwamanda Adam Umar Omajido ya fara ne da godiya ga Allah madaukakin Sarki tare da jinjina ga Malamai da Sarakunan da suke zaune a wajan wannan taro.

Bayan haka ya ce, Gaskiya da taimako al'umma ne yasa Kwamandar Nigerian Neighborhood Watch Tafa Adam Umar Omajudo ya sami wannan lanbobin yabo a gida da waje.

Farfesan ya kara da cewa  dukkan wadannan kungiyoyi ba su san Adam ido da ido ba amma suna jin kokarin da yake yi a jihar Kaduna da kasa baki daya a bangaren tsaro da samawa matasa abin yi.

Farfesa ya ce bisa irin wannan hidima da wannan bawan Allah yake yi wasu a boye yake yi wasu a fili yake yi bisa haka ne wannan gamaiyar kungiyoyi dake gabatar da ayyukansu a wannan kasa Nijeriya da sauran kasashe na duniya baki daya suka ga ya kamata su kara mashi kwarin guiwa tare da nuna mashi abin alherin da yake yi duniya tana gani kuma suna yabawa.

Bayan dogon jawabi da Farfesan ya yi karshe ya yi godiya da yabo da Malamai da Sarakunan da suka sami damar zuwa wajan.

Alhaji Ibrahim Musa Dan Kwairo wanda shi ne Uban taro kuma mai masaukin baki kuma shugaba ga wanda aka taru dominsa shima a nasa jawabin yayi godiyane ga kungiyoyi.

Karshe yaja kunnen kwamandar da cewa kar ya canza daga tarbiyar da suka bashi yace hakan zai kara mashi daraja da daukaka a cikin mutane.

Dakta Ubale mai maciji ma yayi jawabin nuna jin dadinda a matsayin abokin aikinsa yace, tabbasa Omajido mutumne mai taimako da tausayin al'umma don haka yace son gode da karamcin da akayi masa.

Bayan jawaban manya ne aka mikawa kwamandan kanbunan karamcin kusan guda 12 wanda hakan ya zama abin alfari ga abokansa da yan'uwa na jini.

A nasa jawabin Kwamandan Ambassador Adam Umar Omajido ya nuna jin dadinda sosai yace hakan ya bashi kwarin guiwa kuma yayi fatan alherin ga gamaiyar kungiyoyi da suka karramashin kuma ya tabbatar da cewa abin arzukin da mahifinsa ya dorasu akaine ke dawowa akan rayuwarsu a halin yanzu yace tabbas bin iyayi ne ya jawo masa wannan karamcin don haka yayi fatan alherin ga dukkan bakin da suka sami zuwa na nesa dana kusa kuma yayi godiya ga Uban gidansa Alhaji Ibrahim Musa Dan kwairo bisa shawara da ya kan dorashi akai 

Kuma ya jinjinawa sauran jami'an tsaro da suke aikin taimakawa jama'a dare da rana yayi fatan Allah ya mayar da kowa gida lafiya.

Bayan an mika kambun ga mai kwamandar ne sai aka baiwa mawakan zamani lokaci suka nishadantar da mahalarta taron daga cinkin mawakan akwai Sanibraza da dai sauransu

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments