Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Champions League: Salah Ya Samu Abin Da Yake So Bayan Madrid Ta Doke Man City

  Burin ɗan wasan gaba na Liverpool da Masar Mohamed Salah ya cika bayan Real Madrid ta cinye Manchester City a daren Laraba, inda ta kai wa...

 


Burin ɗan wasan gaba na Liverpool da Masar Mohamed Salah ya cika bayan Real Madrid ta cinye Manchester City a daren Laraba, inda ta kai wasan ƙarshe a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Madrid ta doke City ne yayin wani ƙayataccen wasa a filin wasa na Santiago Bernabeu da ya tashi 3-1 - wato 6-5 gida da waje.

Yanzu Madrid za ta fafata da Liverpool a wasan ƙarshen a birnin Paris na Faransa bayan ita ma ta doke Villarreal ranar Talata, kuma da ma abin da Salah yake so kenan.

"Ina so na haɗu da Madrid," in ji Salah jim kaɗan bayan tashi daga wasansu da Villarreal.

"Idan zan faɗi gaskiya, City ƙwararriyar ƙungiya ce, mun yi wasa da su a kakar nan ba sau ɗaya ba. Amma idan ka tambaye ni na fi son Madrid," kamar yadda ya faɗa wa BT Sport.

A wani saƙo kuma da ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan tashi daga wasan na Real, Salah ya aike da saƙon cewa "akwai jiƙaƙƙiya tsakaninmu", wanda ake ganin da Madrid yake.

Wasan dama ce da Liverpool za ta samu don ɗaukar fansa a kan Real Madrid bayan abin da ya faru a wasan ƙarshe shekara huɗu da suka wuce a birnin Kiev, inda aka tilasta wa Salah fita daga wasan yana hawaye bayan ya ji rauni sakamakon arangamar da suka yi da Sergio Ramos.No comments