Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dakatar Da Zaben Kungiyar NUJ A Zamfara Akwai Lauje Cikin Nadi - 'Yan Takara

Daga Hussaini Ibrahim Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawallen Maradun ta dakatar da zaben 'ya&#...Daga Hussaini Ibrahim

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawallen Maradun ta dakatar da zaben 'ya'yan  kungiyar 'yan jarida reshen Jihar Zamfara watau NUJ da Kungiyar za ta gabatar a ranar Alhamis mai zuwa a Gusau babban birnin Jihar Zamfara saboda rashin tsaro.

Babban Sakatare na ma'aikatar yada labarai na Jihar, Barista Sani Nasarawa ya bayyana hakan ne a takardar da ya sanya ma hannu ya aikawa jami'an tsaron da Uwar Kungiyar NUJ ta kasa a Gusau babban birni Jihar Zamfara.

Tunda farko an shirya gudanar da zaben a ranar 14 ga Afrilu, 2022 amma Uwar kungiyar ta kasa, NUJ ta maida shi baya saboda wasu dalilai zuwa ranar 12 ga Mayu, 2022.

A cewar sanarwar, lokacin da aka sanya  bai dace ba saboda matsalar tsaro da jihar ke fama da shi, inda ta kara da cewa, ma’aikatar yada labaran jihar za ta tuntubi jami’an tsaro domin sanya rana da lokacin da ya dace domin gudanar da zaben.

Haka kuma an mika wannan takarda ga shugaban Kungiyar ta Kasa da kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara da Daraktan tsaro na jihar, da kuma Kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta kasa reshen jihar Zamfara.

Idan ba a manta ba cikin mako guda an sami yawaitar kai hare-hare cikin wasu kananan hukumomi inda aka kashe mutane sama da sittin, a yayin da hakan ya sanya Gwamnatin Jihar zamfara har ta kai daukin gaggawa na abinci da kudade. ga al'ummar da masifa ta safa.

Wakilinmu ya tuntubi 'yan takarar akan dakatar da zaben, sun bayyana masa cewa, akwai Lauje cikin nadi don yan takarar da suka fito hazikai ne jajirtattu wajen ganin 'yan Kungiyar sun samu ci gaba ta kowanne bangare, kuma sun tabbatar masu da cewa, ba za su dauki wulakanci ba daga kowane wajen tafiyar da aikinsu na Jarida, kuma gwamnati ta makara wajen sai ma dan takara fam na zaben dan ganin ita ke da wuka da nama kuma duk hanyar da za ta bi na ganin a kara wa'adin saida fam dan Dan takara gwamnatin ya saya abin yaci tura, shi ne ya sanya ta yi amfani da matsalar tsaro ta dan dakatar da zaben kungiyar da membobinta ba su wuce 200 ba. Amma idan ta tashi taronta da dubun-dubatar mutane na siyasa mantawa take da Tsaro sai na 'yan jarida.

No comments