Shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University dake Maradi a Jamhuriyar Nijar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya buka...
Shugaba
kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University dake Maradi a
Jamhuriyar Nijar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bukaci daliban Jami’ar da ke
karatun kimiyyar gwaje-gwaje da su koyi ilimin harsuna da dama domin samun
damar cin gajiyar ayyukan yi da ake da su a fadin duniya baki daya.
Farfesa
Gwarzo ya yi wannan kiran ne a yayin bikin rantsuwar daliban kimiyyar dakin
gwaje-gwajen karo na 7 wanda kungiyar likitocin gwaje-gwaje ta Nijeriya wato ‘The
Medical Laboratory Science Council of Nigeria’ a turance ta gudanar a birnin
Tarayya Abuja.
Cikin
dalibai 383 da aka yaye daga Jami’o’i daban-daban a fadin duniya, Jami’ar
Maryam Abacha American University, dake Maradi ta kwashi kashi 50 cikin 100 cikin
wadanda aka rantsar da su a kungiyar.
Farfesa
Gwarzo wanda shi ne babban bako na musamman a wajen taron, ya kuma jaddada
bukatar su na kasancewa jakadu nagari ga Jami’o’insu da ma kasar baki daya a
duk inda suka samu kansu.
A
yayin da yake yabaw jajircewa da kuma adalcin shugabancin kungiyar likitocin dakin
aikin gwaje-gwaje ta Nijeriya kan kwarewarsu, Farfesa Gwarzo ya kuma godewa
gwamnatin Tarayya bisa samar da yanayi mai kyau.
A
cikin jawabinsa, Magatakardar Kungiyar, Dakta Toman Erhabor ya bayyana Kimiyyar
gwaje-gwaje a matsayin wata kwararriyar fasaha mai tasirin gaske da aka tsara domin
samar da babban tushe na ilimin kimiyya da kuma amfani da shi a cikin tsarin
kiwon lafiya.
Erhabor
ya bayyana cewa rantsuwar zai bai wa daliban da suka kammala karatun digirinsu
a bangaren kimiyyar gwaje-gwaje dama a cikin aikace-aikacen da suka da hada da fannin
likitanci, masana'antar harhada magunguna, cibiyoyin bincike, masana'antar
abinci da kuma kayan bincike da kera injina.
Ya
kuma bukaci kungiyar da ta dauki nauyin daukar dalibai ‘yan kasashen waje dari
uku da tamanin da uku tare da yin kira a gare su da su ci gaba da nuna kwarewa
wajen bunkasa bangaren.
Shugaban
kungiyar ya yabawa Jami’ar Maryam Abacha American University, Maradi bisa yadda
take nuna kwazo a bangare ilimi tare da yin kira ga sauran Jami’o’in Afirka
masu zaman kansu da su yi koyi da Jami’ar domin bunkasa ilimi.
No comments