Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Fasto Ya Caji Mutane Dala 700 A Matsayin Kudin Kai Su Aljannah

  A wani abu kamar almara, wani limamin Kirista a Najeriya, Fasto Ade Abraham ya bukaci mabukata zuwa Aljannah da su biya shi naira 310,000 ...

 


A wani abu kamar almara, wani limamin Kirista a Najeriya, Fasto Ade Abraham ya bukaci mabukata zuwa Aljannah da su biya shi naira 310,000 ko kuma Dala 750 domin nuna musu hanyar da za ta kaisu cikin ta.

Wani daga cikin mabiyan sa ne ya kai kara tashar ‘Yan Sanda saboda abinda ya kira yaudarar da Fasto Abraham ya masa na karba wadannan makudan kudade a Araromi-Ugbeshi dake Jihar Ekiti ba tare da nuna masa hanyar zuwa Aljannar ba.

Faston yace tabbas yayi wannan ikrari domin kuwa Ubangijin sa ne ya umurce shi domin gwada mabiyan sa, amma kuma yace shi bai karbi kudi daga hannun wani ba.

Tuni kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Jihar Ekiti ta fitar da sanarwar nesanta kanta daga Fasto Abrahma da matakan da yake dauka, yayin da Yan Sanda suka tattara shaidu daga mabiya faston a binciken da suke gudanarwa.

Rahotanni sun ce limamin Kiristan ya fara kafa mujami’ar sa ce a Jihar Kogi daga bisani ya koma Jihar Kaduna kafin yayi kaura zuwa Jihar Ekiti.

No comments