Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Fatuhu Muhammad Da Ya Ce A Cefanar Da Jami'o'i Ya Fadi Takarar Fidda Gwani

Fatuhu Muhammad da ke wakiltar Daura/Sandamu/Maiadua a Majalisar Tarayya, ya sha kaye a hannun masu zaben fid da gwani da aka yi jiya Juma&#...


Fatuhu Muhammad da ke wakiltar Daura/Sandamu/Maiadua a Majalisar Tarayya, ya sha kaye a hannun masu zaben fid da gwani da aka yi jiya Juma'a. 

Muhammad, wanda dan uwan Buhari ne, ya sha kaye ne a hannun Aminu Jamu a kokarinsa na yin tazarce a karo na biyu. 

Fatuhu Muhammad a majalisar wakilai ya taba kai kudurin a cefanar da jami'o'i mallakin gwamnatin Nijeriya su koma hannun 'yan kasuwa. 

A lokacin da yake sanar da sakamakon zaben jiya Juma'a, jami'in zaben, Bala Zango ya bayyana cewa Aminu Jamu ya samu kuri'u 117, wanda ya sa ya doke abokin karawsrsa da ya tsira da kuri'u 30 . 

A watan Oktoba 2018 ne 'yan takara uku suka fito neman wannan kujera ta mazabar Daura/Sandamu/Maiadua, amma aka da kara Muhammad a kansu saboda lokacin Buhari da dan'uwana Mamman Daura sun daura masa gindi.

A wancan lokacin' 'yankarar uku; Salisu Daura, Aminu Jamu da Kabir Abdullahi, sun yi Allah wadai da irin rashin adalci, bambanci da bangarencin da suka ce gwamnatin Jihar Katsina ta nuna masu a lokacin. 

Muhammad shi ne mutum na biyar da ke da alaka ko kusanci da Muhammadu Buhari da suka rasa kujerunsu a zabukan nan, baya ga Bashir Ahmad da Sha'aban Sharada a Kano,  Sani Sha’aban a Kaduna da kuma Gudaji Kazaure a Jihar Jigawa.

No comments