Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Guguwar Yashi Ta Jikkata 'Yan Iraqi Dubu Biyar

  Mutum guda ya rasa ransa, yayin da aka garzaya da wasu akalla dubu biyar zuwa asibiti a Iraqi, bayan kamuwa da cutar sarkewar numfashi a r...

 


Mutum guda ya rasa ransa, yayin da aka garzaya da wasu akalla dubu biyar zuwa asibiti a Iraqi, bayan kamuwa da cutar sarkewar numfashi a ranar Alhamis, sakamakon guguwar yashin da ta afkawa sassan kasar, wadda ita ce ta bakwai da ta auku a makwannin baya bayan nan.

Mazauna larduna shida daga cikin 18 na kasar Iraki suka ciki har da Bagadaza ne da kuma yankin Al-Anbar da ke yammacin kasar suka sake tsintar kansu lullube da katafaren gajimare na kura da ya mamaye sararin samaniyarsu.

Hukumomin lardunan Al-Anbar da Kirkuk da ke arewacin babban birnin Iraqi sun bukaci jama'a da su kasance a gida, domin kare rayukansu.

Wani jami’in kiwon lafiya a daya daga cikin asibitocin lardin Al-Anbar Anas Qais, ya ce kawo yanzu sun karbi majinyata sama da 700 da ke fama da matsalar numfashi.

A lardin Salaheddin da ke tsakiyar kasar ta Iraqi kuwa, jami’ai sun ba da rahoton cewa akalla mutane 300 suka kamu da cutar matsalar numfashin, yayin da lardunan Diwaniya ta tsakiya da kuma lardin Najaf da ke kudancin Bagadaza, kowanne ya samu mutane kusan 100-100 masu fama da matsalar numfashin saboda guguwar yashin.

Iraqi na fuskantar matsalar sauyin yanayi musamman ganin yadda aka samu karancin ruwan sama da yanayin zafi a cikin 'yan shekarun da suka gabata.

Masana dai sun ce wadannan abubuwa na barazanar kawo bala'in zamantakewa da tattalin arziki a kasar da ke kokarin murmurewa daga yakin da ta sha fama da shi.

A watan Nuwamba, Bankin Duniya ya yi gargadin cewa Iraqi na iya fuskantar raguwar albarkatun ruwa da kashi 20 cikin 100 nan da shekarar 2050 saboda sauyin yanayi.

A farkon Afrilu, wani jami'in gwamnati ya yi gargadin cewa kasar na iya fuskantar kwanaki 272 na kura a duk shekara cikin shekaru masu zuwa, yayin da ma'aikatar kula da muhalli ta ce za a iya magance lamarin ta hanyar kara yawan ciyayi da kuma samar da dazuzzukan da za su yi aikin tare karfin guguwar ta Yashi.

No comments