Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gumi Ya Sharwaci Gwamnati Ta Biya Kudin Fansar Fasinjojin Jirgin Kasan Da Aka Yi Garkuwa Da Su

  Shahararren malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta biya ‘yan ta’adda kudin fansa don fanso...

 


Shahararren malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta biya ‘yan ta’adda kudin fansa don fanso fasinjojin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna su 62 da ake garkuwa da su.

Ya bayyana haka ne a yayin addu’o’i na musamman da Jam’iyyar Matan Arewa ta shirya don wadanda ake garkuwa da su.

A ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasa dauke da fasinjoji  da ke kan hanyarsa ta zuwa kaduna daga Abuja.

Gumi ya ce ‘yan siyasa na daukar kudi har sama da Naira miliyan 25 don sayen tikitin takara, a maimakon biyan kudin fansa don ceto wadanda ake garkuwa da su.

A jawabinsa, shugaban kungiyar Kiristoci na duniya CAN, Reverend Joseph Hayab ya kalubalanci shugabanni su yi abin da ya dace wajen tabbatar da dawowar wadanda aka yi garkuwa da su.

No comments