Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Birtaniya Ta Kwato Karin Dala Miliyan 23.4 Da Abacha Ya Sace

  Hukumar da ke yaki da masu aikata laifuka ta kasa (NCA) a kasar Birtaniya ta ce ta kwato dala miliyan 23, 439, 724.98 da ake kyautata zato...

 


Hukumar da ke yaki da masu aikata laifuka ta kasa (NCA) a kasar Birtaniya ta ce ta kwato dala miliyan 23, 439, 724.98 da ake kyautata zaton wasu makusanta da iyalan tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha ne suka sace daga Nijeriya a shekarun 1990.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Alhamis, an ce kudaden sun kasance wani bangare ne na wasu makudan kudade da ma’aikatar shari’a ta Amurka (USDOJ) ta bayyana cewa Abacha da abokansa ne suka karkatar da su.

NCA ta bayyana cewa yanzu haka an tura kudaden zuwa Ofishin Cikin Gida don mikawa ga USDOJ.

Har ila yau, kusan shekaru bakwai ke nan ana bibiyar shari'ar da aka tsawaita tare da tattaunawar kasa da kasa domin samun odar dawo da kudaden, tare da aiwatar da odar kwacen ta Amurka da ta shafi kudaden da aka kwato.

Babban Manajan hana Kadarori a NCA, Billy Beattie, ya ba da tabbacin yakin da hukumar ke yi da ayyukan halasta kudaden haram a Birtaniya.

"Hukumar NCA ta himmatu wajen tabbatar da cewa Birtaniya ba mafaka ce ga masu aikata laifuka ba don yin amfani da kudaden da suka samu daga aikata laifuka, kuma kwato kadarori na daga cikin babban makami mai karfi a wannan yaki," in ji Betie.

"Muna aiki kafada da kafada da Birtaniya da abokan hulda na kasa da kasa don tunkarar barazanar da cin hanci da rashawa ke haifarwa, wanda ke yin illa ga matalauta da kuma marasa galihu a cikin al’umma.

"Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa masu cin hanci da rashawa ba su amfana da ayyukansu ba."

Ana ci gaba da gudanar da shari’ar NCA inda USDOJ ta gano cewa Abacha da mukarrabansa sun karkatar da wasu kudade.

Rahotanni sun ce tun bayan mutuwar Abacha a 1998, kudaden da aka kwato an ajiye su a manyan kasashe hudu: Switzerland, Jersey Island a Birtaniya, Amurka, da kuma Liechtenstein.

A lokacin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar a shekarar 1999, an kwato dala miliyan 750 a yayin da aka kwato dala biliyan 1.2 a shekarar 2002; an kuma dawo da Dala miliyan 149 daga tsibirin Jersey, dake Birtaniya a 2003; Dala miliyan 500 kuwa an kwato a shekarar 2004 daga kasar Switzerland, sannan an kwato wasu dala miliyan 458 a shekarar 2005 daga kasar Switzerland, dukkansu a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Haka kuma gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta kwato dala biliyan 1 a shekarar 2012 da dala miliyan 380 a shekarar 2015, dukkansu daga kasar Switzerland.

Hakazalika, Liechtenstein da Amurka sun dawo da dala miliyan 227 da dala miliyan 48 a shekarar 2014 a lokacin gwamnatin Jonathan.


No comments