Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hadimin Shugaba Buhari, Ya Sha Kaye A Zaben Fidda Gwani Na APC

  Tsohon Mai taimaka wa Buhari a kan kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad ya sha Kaye a Zaben Fidda Gwani da jam'iyar APC ta gaba na ...

 


Tsohon Mai taimaka wa Buhari a kan kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad ya sha Kaye a Zaben Fidda Gwani da jam'iyar APC ta gaba na Majalisar Tarayya a mazabar Gaya/Ajingi/Albasu

 Dan Majalisar Wakilai mai ci, Abdullahi Mahmud Gaya ya daga Bashir Ahmad sama kafin ya tikashi ga kasa inda ya samu nasara da kuri'u 109, yayin da Bashir Ahmad ya tashi da kuri'u 16.

Sai bayan Sakamakon Zaben Bashir Ahmad ya jingine wani sako a shafinsa na Twitter inda ya ce ya fice daga wajen zaben ne bayan ya fahimci ana barazana ga rayuwarsa da masu zaben sa. 

Wani abin mamaki shi ne yadda hatta abokanan aikinsa da suka shekara 7 a Villa tare Kamar sunyi farin ciki da kayen da ya Sha daga wani sakon da suka wallafa a Shafin Facebook na Buhari Reporters.

No comments