Honorabul Muktar Isa Hazo Ya Amsa Kiran Al'umma Na Tsayawa Takara A Karo Na Uku


Daga Idris Umar, Zariya

A yau ne 15/5/2021 Dan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar gundumar Basawa a karamar hukumar Sabon Gari Zariya ta jihar Kaduna, Honorabul Muktar Isa Hazo (Kenzy) ya gabatar da kansa a matsayin dan takarar kujeransa karo na 3 a ofishin jam'iyyarsa ta APC na karamar Hukumar Sabon Gari.

Ya zanta da manema labarai game da amincewarsa da kiran da al'ummar gundumarsa suka yi masa na kara dawowa karo na uku a halin yanzu.


Post a Comment

0 Comments