Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

"Idan An Kashe Mu Mun Yi Shahada", Inji Matasa Masu Zanga-zanga A Sakkwato

A yau Asabar gungun matasa a garin Sakkwato suka fito zanga-zangar adawa da kama matasan da ake zargin sun kashe tare da kona ga...


A yau Asabar gungun matasa a garin Sakkwato suka fito zanga-zangar adawa da kama matasan da ake zargin sun kashe tare da kona gawar Deborah, dalibar Kwalejin Ilimi ta Sakkwato wacce ta yi kalaman batanci ga fiyayyen halitta Manzon Rahama (SAWW). 

Sai dai a yayin zanga-zangar matasan sun nufi gidan Sarkin Musulmi suna rera wakar 'LABBAIKA YA RASULILLAH' 'LA'ILAHA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULILLAH', sai dai wasu ganau sun ce matasan sun rika jifa a gidan Sarkin Musulmin Nijeriya, Sultan Sa'ad Abubakar Na III, hakan yasa jami'an tsaro suka bude wuta kan masu zanga-zangar da harsasai masu rai tare da antaya barkonon tsohuwa. 

Sai dai wakilinmu a Sakkwato ya shaida mana cewa matasan sun rika cewa ko jami'an tsaron sun kashe su shahada suka yi.

Ya zuwa yanzu kamar yadda Jaridar MADOGARA ta tabbatar jami'an tsaron sun raunata mutum biyu. 

Hotunan wadanda aka raunata

No comments