Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

INEC Ta Gargadi Jam'iyyun Nijeriya Kan Jinkirta Fidda Gwani

  Hukumar Zabe a Najeriya ta gargadi Jam’iyyun kasar da su tabbatar da kammala zaben fidda gwani na Yan takarar zabe mai zuwa a cikin wata g...

 


Hukumar Zabe a Najeriya ta gargadi Jam’iyyun kasar da su tabbatar da kammala zaben fidda gwani na Yan takarar zabe mai zuwa a cikin wata guda, ko kuwa ta haramta musu tsayar da Yan takarar.

Daraktan wayar da kan jama’a dangane da shirin zaben Festus Okoye ya bayyana haka, inda yake cewa tun daga ranar 26 ga watan Fabarairu suka gabatar da shirin zaben shekarar 2023 wanda ya umurci jam’iyyun da su gudanar da zaben fidda gwani tsakanin ranakun 4 ga watan Afrilu zuwa 3 ga watan Yunin wannan shekara.

Okoye ya ce bisa wannan jadawali, duk wani zaben fidda gwanin da akayi bayan wadannan ranaku ya zama haramcacce, kuma hukumar ba zata amince da shi ba.

Daraktan yace sun shaidawa daukacin Jam‘iyyu 18 dake da rajista wannan doka kamar yadda Sashe na 82 na Dokar Zaben shekarar 2022 ya tanada.

Okoye yace tuni wasu daga cikin jam’iyyubn suka fara shirin aiki da dokar, kuma Hukumar zabe ta tura jami’an ta domin sanya ido akan yadda suke gudanar da zaben.

Idan dai ba’a manta ba, sabawa dokar zabe wajen gudanar da zaben fidda gwani ya sa Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta rasa kujerar gwamna da Yan majalisun tarayya da na jiha a zaben shekarar 2019.

No comments