Jagoran Iran Ya Yi Wa Fursunoni 1,542 Afuwa Albarkacin Ramadan

 


Jagoran Juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi afuwa ko sassauta hukuncin ɗauri ga fursunoni 1,542 da aka yanke wa hukunci a wani mataki na murnar bikin Sallah da ke nuna kawo ƙarshen azumin watan Ramadan, kamar yadda shafinsa ya bayyana a ranar Asabar.

Ayatollah Ali Khamenei ya ce “ya amince da yin afuwa ko sassauta hukuncin da aka yanke wa masu laifi 1,542."

Jagoran yakan yi afuwa ga masu laifi a manyan bukukuwan addini, tare da sa hannun shugaban ɓangaren shari’ar ƙasar

A ranar Litinin ne za a yi bikin Sallah a Iran.


Post a Comment

0 Comments