Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam, JNI reshen karamar hukumar Zaria ta maka Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli a kotu bisa za...
Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam, JNI reshen karamar hukumar Zaria ta maka Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli a kotu bisa zarginsa da karkatar da cekin kuÉ—i na naira miliyan 20 da ma’aikatar Sufuri ta Tarayya ta ba ta.
JNI ta ce an biya cekin cekin ne ga kungiyar a matsayin diyyar karÉ“e filinta na Kwalejin Larabci ta Jama’atu, É“angaren maza, domin aikin hanyar jirgin Æ™asa na Kaduna zuwa Zariya a wani É“angare na aikin titin jirgin Æ™asa daga Ibadan zuwa Kano.
A karar da aka shigar a ranar 25 ga watan Afrilu, a babbar kotun jihar Kaduna, shugaban ƙungiyar da sakataren JNI reshen Zazzau, Zaharadeen Maccido da Usman Maccido, sun bukaci a saki cakin ɗin.
Masu shigar da ƙara sun yi ikirarin cewa Sarkin ya rusa shuwagabancin JNI ne a matsayin wata hanya ta rufe musu baki kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta labarto.
No comments