Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) da ke Kano, ta sanya wa Makarantar Kwamfuta sunan Ministan Sadarwa da Tattal...
Jami’ar Maryam Abacha
American University ta Nijeriya (MAAUN) da ke Kano, ta sanya wa Makarantar Kwamfuta
sunan Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani na Nijeriya, Farfesa Isa
Ali Ibrahim Pantami.
Shugaban Jami’ar kuma
wanda ya kafa Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya shaida wa PRNigeria
cewa matakin na daya daga cikin kokarin da Jami’ar ta ke yi na ganin ta shaida
bajintar da Farfesa Pantami ya yi a matsayin minista a majalisar shugaban kasa
Muhammadu Buhari.
“A matsayinsa na ma’aikacin
da ya biya hakkinsa a aikin gwamnati kuma wanda ya kawo sauyi ga tattalin
arzikin kasar nan ta fuskacin fasaha, tabbas ya cancanci masu tasowa su yi koyi
da shi, a don haka kasancewarsa a fannin da ya yi fice a cikinsa, mun ga ya
dace mu sanya wa makarantarmu ta kwamfuta sunansa." Gwarzo yace.
MAAUN jami'a ce mai
zaman kanta da ke cikin tsohon birnin Kano, wacce aka sadaukar domin samarwa É—alibai
mafi kyawun ilimi, zamantakewa da gogewa.
Makarantar ta kwamfuta
tana ba da kwas a bangaren Tsaron Intanet (Cybersecurity), Fasahar Sadarwa (Information
Technology), Injiniyan Software (Software Engineering) da Kimiyyar Kwamfuta (Computer
Science).
Idan za ku iya tunawa a
watan Fabarairu, Kamfanin Image Merchants Promotions Limited (IMPR), mawallafan
PRNigeria da Economic Confidential sun kafa taron bayar da lambar yabo na
shekara-shekara ga mafi kwazon daliban da suka kammala karatun digiri na farko
a fannin hulda da jama'a da tattalin arzikin zamani (Digital Economy) a Jami'ar
Bayero Kano (BUK).
Kyaututtukan wanda aka
sanyawa sunan tsohon shugaban sashen Sadarwa na jami’ar, Farfesa Bashir Ali da
kuma ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Ali Pantami zai shafe
shekaru 10 daga 2022 zuwa 2032 ana gudanar da shi.
An ƙaddamar da
kyaututtukan ne domin ƙarfafawa ɗalibai domin su haɓɓaka sha'awarsu ga aikin sashen
HulÉ—a da Jama'a da kuma bangaren kirkira a ayyukan fasahar zamani waÉ—anda ke da
muhimmanci ga bunkasar tattalin arzikin duniya na yau.
A lokacin da yake
karbar shaidar kudi na Naira Miliyan daya na kyaututtukan a ofishinsa, Mataimakin
shugaban Jami’ar BUK, Farfesa Sagir Adamu Abbas ya yabawa Kamfanin IMPR kan
yadda take gudanar da ayyuka daban-daban na horar da dalibai da matasa da kuma masu
wayar da kan jama’a kan fasahar zamani. Ya kara da cewa za a ba da kyaututtukan
ne ga dalibai na farko a yayin taron da ke tafe na yayen dalibai na shekarar
2022.
Hakazalika, Ma’aikatar
da kuma Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), dukkansu sun samu
lambar yabon 2022 SABER African PR Certificate of Excellence.
Kyautar PR din na
shekara-shekara na African PR na shaida nasarori da kuma hulda (SABRE) Kamfanin
Provoke Media (Holmes Report a da) tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Hulɗa da
Jama'a ta Afirka (APRA) ke shirya taron.
Za a yi bikin bayar da
kyautar ne a Dar es Salaam, Tanzania a ranar 25 ga watan Mayu, a wani bangare
na taron hulda da jama'a na Afirka na 2022.
No comments