Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jihar Edo Za Ta Fara Biyan N40,000 Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnan Jihar Edo da ke kudancin Najeriya, Godwin Obaseki, ya ƙara albashi mafi ƙaranci a jihar zuwa N40,000 sama da N30,000 da gwamnatin ta...


Gwamnan Jihar Edo da ke kudancin Najeriya, Godwin Obaseki, ya ƙara albashi mafi ƙaranci a jihar zuwa N40,000 sama da N30,000 da gwamnatin tarayya ta saka wa ma'aikatanta.

Obaseki ya sanar da ƙarin a yau Lahadi yayin da ake bikin Ranar Ma'aikata ta Duniya. Kazalika wasu rahotanni na cewa tsoffin ma'aikatan jihar sun gudanar da zanga-zangar neman a biya su garatutinsu a yau ɗin.

"Kamar yadda muka sani, mafi ƙarancin albashi na N30,000 da ƙyar zai iya riƙe iyali, rashin ɗa'a ne da tausayi mu ci gaba da basarwa cewa ba mu san halin ƙunci da ma'aikatanmu ke ciki ba," a cewar Mista Obaseki.

"Gwamnatin Edo ta yanke shawarar sake duba albashi mafi ƙaranci daga N30,000 zuwa N40,000 kowane wata, ba wata tantama Edo ce jiha ta farko tun bayan shigowar annoba (korona) da ta ɗauki wannan matakin."

'Yan Najeriya na ci gaba da fama da hauhawar farashin kayayyaki yayin da hukumar ƙididdiga ta NBS ta ce hauhawar farashi a watan Maris ta kai kashi 15.9 cikin 100.

No comments