Komai Zai Yi Daidai A Nijeriya -Obasanjo Ya Yi Wa Nijeriya Fatan Alheri


Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo ya baiyana ƙwarin gwiwa cewa duk da ɗumbin matsalolin da ke damun Nijeriya, komai zai zama tarihi.

Obasanjo ya baiyana hakan ne a wani taron addini na ƴan ɗariƙar Deeper Life a birnin Abeokuta a ranar Talata, wanda ya halarta ta yanar gizo.

Obasanjo ya yi kira ga al'ummar Nijeriya da su koma ga Allah domin samun sauƙin matsalolin da su ke damun ƙasar.

A cewar Obasanjo, duba da irin matsalolin da Nijeriya, Afirka da ma su iya ke ciki, babu abinda mu ke buƙatar sai taimako da ga Ubangiji.

Ya yi kira ga al'umma da su sa imani da Allah a ransu da kuma neman taimakon sa domin Ya yaye matsalolin.

Post a Comment

0 Comments