Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Nemi A Biya Naira Miliyan 100 Kafin Su Sako Jaririya

Daga I. Umar Kaduna Yau kwana 35 wannan jaririyar tana hannun masu garkuwa da mutane. Ita yaririyar an haifeta  da kwana 5 ne sa...Daga I. Umar Kaduna

Yau kwana 35 wannan jaririyar tana hannun masu garkuwa da mutane.
Ita yaririyar an haifeta  da kwana 5 ne sai masu garkuwa da mutane suka shiga har cikin gida suka dauketa a hannun mahaifiyarta. 

Wani daga cikin masu garkuwa da mutanen sai tausayi ya kama shi ya ce gaskiya a hada harda uwarta inda nan take suka tasa keyar Uwar jaririyar tana cikin jego kwana 5 da haihuwa haka suka tasa keyar ta suka nufi daji da ita bayan sun hada mutane 5 a cikin gidan. 

Wata majiya ta ce masu garkuwa da mutanen sun kira dangin mai jegon bayan 'yan kwanaki da cewa suna neman Naira Milyan 100 kafin su sako jaririn da Uwar jaririn.

Bisa haka ne Jaridar MADOGARA ta yi takakkiya ta ziyarci dangin mai jegon don jin masu jaje tare da jin ko wani hali ake ciki zuwa yanzu kwanaki 35.

Tuni suka ce har yanzu ba labarin sako wannan jaririyar da sauran wadanda aka yi garkuwan da su.

Don haka suke rokon al'umma da su taimaka masu da addu'o'i kuma sun roki  gwamnati ta taimaka masu kamar yadda aka taimakawa wasu da irin wannan jarabawar ta afka masu.

Bincike ya tabbatar da cewa maharan sun kwashe akalla mutane 6 ne a gida daya duk da jaririyar.

Wannan lamarin ya faru ne a wata Anguwa da ake kira Sabuwar Abuja dake a garin Giwa a jihar Kaduna. 

Ya zuwa hada wannan labarin jama'a na ta nuna alhini da damuwarsu ga dangin mai jegon da sauran mutanen da aka kwashen.

No comments