Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MDD Ta Kaddamar Da Bincike A Kan Zargin Cin Zarafin Da Ake Wa Rasha

Kwamitin Kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya amince da kaddamar da bincike kan wasu manyan laifukan cin zarafin da sojojin R...Kwamitin Kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya amince da kaddamar da bincike kan wasu manyan laifukan cin zarafin da sojojin Rasha ke aikatawa a Ukraine.

‘Yan majalisar 33 suka kada kuri’ar amincewa da bukatar gudanar da bincike kan laifukan da ake zarginsu da aikatawa, da nufin hukunta wadanda suka aikata su.

Sai dai kasashen China da Eritriya sun kada kuri'ar kin amincewa da kudurin, yayin da kasashe 12 ciki har da Indiya da Pakistan da kuma Cuba suka kaurace wa zaben.

Rasha ta ki halartar taron bisa dalilan ta na cewa siyasa ce a cikin sa.

Mataimakiyar ministar harkokin wajen Ukraine Emine Dzhaparova ta tabbatarwa majalisar cewar dakarun na Rasha sun yi wa wani yaro dan shekara 11 fyade a gaban mahaifiyarsa, lamarin da ta bayyana a matsayin mugunta.

A dai ranar 24 ga watan Fabrairun da ya gabata ne Rasha ta kaddamar da hari a Ukraine, inda a ranar 4 ga watan Maris kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkun duniya ya kaddamar da kwamitin bincike a kan zargin cin zarafin da Rasha ke yi a Ukraine.

No comments