Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mu Na Maraba Da Kowa A NNPP -Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce jam'iyar NNPP na maraba da kowa, inda ya ce kofa a buɗe ta ke ga...Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce jam'iyar NNPP na maraba da kowa, inda ya ce kofa a buɗe ta ke ga duk mai sha'awar shiga. 

Kwankwaso ya faɗi haka ne yayin da a ke raɗe-raɗin cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, da sauran ƴan jam'iyar APC na shirin sauya sheƙa zuwa NNPP.

Da ya ke zanta wa da Freedom Radio a jiya Talata a Abuja, Kwankwaso ya ce ba zai yi wu a ce dole sai masoya ne za su shiga jam'iyar ba.

A cewar sa, ko waɗanda a ka samu saɓani da su a baya, kuma su ka nuna sha'awar shigo wa jam'iyar, to kofa a buɗe ta ke.

Ya ƙara da cewa ko ma da wacce irin buƙata mutum ya shigo jam'iyar, to za a zauna a ga irin tsare-tsaren da za a yi domin a biya wa kowa hakkin sa.

"Ko ƴan G-7 ma muna maraba da su domin su ma ba sa jin daɗin abubuwan da su ka faru a jihar Kano a shekaru bakwai da su ka wuce.

"In dai dama mu na son NNPP ta girma ta kuma yaɗu, to dole a baiwa kowa damar ya shiga jam'iyar," in ji Kwankwaso.

No comments