Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

PDP Ta Sauya Ranakun Gudanar Da Zaɓukan Fid Da Gwani

  Kwamitin Gudanarwa na jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ya ɗage lokutan da ya shirya gudanar da wasu zaɓukan fid da gwani na jam'...

 


Kwamitin Gudanarwa na jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ya ɗage lokutan da ya shirya gudanar da wasu zaɓukan fid da gwani na jam'iyyar kafin babban zaɓe na 2023.

Wata sanarwa daga Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa Debo Ologunagba ta ce za a gudanar da zaɓukan kujerar gwamna ranar Litinin, 23 ga watan Mayun 2022, yayin da za a yi na sanatoci ranar Asabar, 21 ga Mayun.

Zaɓukan 'yan majalisar wakilai za su gudana ranar Juma'a, 20 ga Mayu, sai kuma na 'yan majalisar jiha da za a yi Laraba, 18 ga watan na Mayu. Haka nan an ɗage taron zaɓar wakilai wato daliget a dukkan ƙananan hukumomi na ƙasa amma sai nan gaba za a faɗi ranar gudanar da su.

Sai dai sauyin bai shafi zaɓen fid da ɗan takarar shugaban ƙasa ba, wanda tun farko aka tsara yin sa ranar 28 zuwa 29 ga Mayu.

No comments