Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rescue Mission Nijeriya Ta Yi Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Yahaya Bello A Kaduna

Daga Aisha Suleiman Zariya Wata kungiyar matasa masu rajin kawo canjin shugabancin Nijeriya a yanzu ta yi gangamin amicewa da Gw...


Daga Aisha Suleiman Zariya

Wata kungiyar matasa masu rajin kawo canjin shugabancin Nijeriya a yanzu ta yi gangamin amicewa da Gwamna Yahaya Bello. 

Taron an gudanar da shi ne a filin motsa jiki na Ploutos dake tsakiyar garin Kaduna.

Kwamared Nasiru Lawal shi ya jagoranci taron ya yi karin haske ga manema labarai a ya yin kammala taron. Ya ce Rescue Nigeria Mission North West ta fito ne kwanta da kwarkwata don nuna goyan baya akan manufar dawo da shugabanci ga hannun matasa don samun ci gaban kasarmu mai albarka.

Kwamared Nasiru ya ce sun ga kyakkyawar misali ga Gwamna Yahaya Bello wajen samawa matasa abin dogaro da kai. Kana ya ce sun shaida kokarinsa a bangaren tabbatar da tsaro a jiharsa.

Gwamna Yahaya Bello matashi ne mai hazaka da sanin darajar matasa don haka suke kira ga matasa su mara wa aniyarsa baya don zai kawo ci gaba ga rayuwar matasa da al'umma baki daya.

Karshe ya nuna jin dadinsa ga miliyoyin matasan jihar Kaduna bisa ba su goyan baya don tabbatar da gangamin cikin tsari da sha'awa kuma ya yi fatan Allah ya koma da kowa gida lafiya.

No comments