Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rikicin Naziru Sarkin Waka Da Nafisa Abdullahi Baban Cinedu Ya Ci Burki

Daga Idris Umar Idan masu bibiyar kafar sada zumunta a yan kwanakinnan yakin baka ya barke a tsakani Naziru  Sarkin waka da Jaru...


Daga Idris Umar

Idan masu bibiyar kafar sada zumunta a yan kwanakinnan yakin baka ya barke a tsakani Naziru  Sarkin waka da Jaruma Nafisa Abdullahi akan maganar Bara da almajiranci a kasar Hausa.

Jaruma Nafisa ta soki iyaye masu barin yaransu suna zuwa bara bisaga yadda barar ta koma a halin yanzu.

Naziru sarkin waka ya yi kutubal da kalaman jaruma Nafisa tare da yin suka mai zafi game da kalaman nata a shafukan sada zumuta.

Wannan lamarin ya ja hankalin al'umma musamma malamai da 'yan siyasa harma da sauran jama'ar gari.

Kusan duk wanda zai magana akan lamarin na su dole ne ya goyi bayan Naziru Sarkin waka ko Jaruma Nafisa.

Hakan yasa da yawan mutane suka zargi Jaruma Nafisa da cewa ta yi wa Almajirai Izgili bisa yadda suka fassara kalaman na ta tare da yi mata tofin ala tsine.

A daya gefen kuma wasu jama'ar sun sa kafa ne suka yi fatali da togiyar da Naziru ya kawo da dake inkarin kalaman Jaruma Nafisa.

Daga cikin jaruman da suka so su tsunduma cikin rigimar akwai jarumi Baban Cinedu mai wasan barkwanci.

Amma sai wasu abu sukai masa burki wanda dole tasa shi ya duro taka a shiga cikin rigimar ta su.

Jaridar MADOGARA ta nemi jin ta bakin Baban Cinedu akan ko me ya sa shi ya tsuke bakinsa akan tataburzar dake tsakanin Sarkin waka Naziru da Jaruma Nasisa Abdullahi?

Sai Baban Cinedu ya ce, " A gaskiya na so daukan mataki amma Naziru nada 'yan'uwa masu mutunci da kima a fuskata bisa irin girma da muke ba juna hakan yasa dole na yi shiru".

Baban Cinedu ya kara da cewa damar kungiyoyin nan ba a sama masu nizami ba wato doka da oda to hakan zai ci gaba da faruwa.

Karshe ya ce samun doka da oda ne zai sanya idan wani ya yi laifi za a iya kirasa a ja mashi kunne da kaucewa matsala irin wacce take faruwa a halin yanzu. 

Kuma ya yi fatan Allah ya hada kan musulmi baki daya. Jaridar MADOGARA ta zanta da shi ne ta wayar salula.

No comments