Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Musulmin Nijeriya Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Dalibar Sakkwato

  Mai Alfarma Sarkin Musulmin Nijeriya Muhammad Saad Abubakar ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa wata dalibar Babbar Kwalejin Ilimin Ji...

 


Mai Alfarma Sarkin Musulmin Nijeriya Muhammad Saad Abubakar ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa wata dalibar Babbar Kwalejin Ilimin Jihar Sokoto da aka zarga da batanci ga Manzon Allah tsira da Amincin Allah suka tabbatar a gare shi.

Wata sanarwar da fadar Sarkin ta gabatar mai dauke da sanya hannun Sakataren Masarautar kuma Danburan din Sokoto, Saidu Muhammadu Maccido ta yi Allah wadai da kisan inda ta bukaci jami’an tsaro da su tabbatar da gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban shari’a.

Masarautar ta bukaci jama’ar Sokoto da kasa baki daya da su ci gaba da zaman lafiya a tsakanin su, yayin da jami’an tsaro ke gudanar da aikin su.

Tuni gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da rufe Kwalejin da kuma kaddamar da bincike akan lamarin kamar yadda kwamishinan yada labarai Isa Bajini Galadanci ya tabbatarwa RFI Hausa.

Rahotanni sun ce wasu fusatattun dalibai ne suka yiwa dalibar Kwalejin da ake kira Deborah duka da kuma cinna mata wuta saboda zargin da suka mata na cin zarafin addinin Islama.

Wani daga cikin daliban Kwalejin ya ce Deborah ta yi kalamun batancin ne a wata kafar sada zumunta da suke amfani da ita, abin da ya haifar da tashin hankalin.

Yanzu haka ana ci gaba da tafka muhawara a kafofin sada zumunta dangane da kisan, inda jama'a ke bayyana ra'ayoyi mabambanta dangane da kisan.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto ta sanar da kama mutane 2 da ake zargin suna da hannu wajen aikata kisan.

 


No comments