Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli ya bada dalilan da su ka sanya ya riÆ™e chekin kuÉ—i har Naira miliyan 20 na Ƙungiyar Jama’atu Nasrul...
Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli ya bada dalilan da su ka sanya ya riÆ™e chekin kuÉ—i har Naira miliyan 20 na Ƙungiyar Jama’atu Nasrul Islam, JNI.
A tuna cewa JNI, reshen Ƙaramar Hukumar Zaria ta maka Sarkin Zazzau É—in a kotu bisa zarginsa da karkatar da cekin kuÉ—i na naira miliyan 20 da ma’aikatar sufuri ta tarayya ta ba ta.
JNI ta ce an biya cekin ne ga kungiyar a matsayin diyyar karÉ“e filinta na Kwalejin Larabci ta Jama’atu, É“angaren maza, domin aikin hanyar jirgin Æ™asa na Kaduna zuwa Zariya a wani É“angare na aikin titin jirgin Æ™asa daga Ibadan zuwa Kano.
A karar da aka shigar a ranar 25 ga watan Afrilu, a babbar kotun jihar Kaduna, shugaban ƙungiyar da sakataren JNI reshen Zazzau, Zaharadeen Maccido da Usman Maccido, sun bukaci a saki cakin ɗin.
Masu shigar da ƙara sun yi ikirarin cewa sarkin ya rusa shuwagabancin JNI ne a matsayin wata hanya ta rufe musu baki.
Sai dai kuma a wata sanrwa da Wazirin Zazzau, Muhammad Inuwa Aminu ya fitar a jiya Laraba ta ce ta riƙe check-in kuɗin ne domin daƙile rikici tsakanin wasu ɓangarori huɗu a cikin JNI ɗin da ko wannen su ke iƙirarin mallakin kuɗin.
"Mu na sane da labaran da a ke yaÉ—a wa ta kafafen sadarwa. Mu na yi wa masoya, Æ´an uwa da abokan arziki bushara cewa za mu zo da bayanai na gaskiya. Gaskiya za ta yi halin ta.
"Sai dai kuma ya kamata jama'a su sani cewa a kwai ɓangarori huɗu a cikin kungiyar JNI ɗin kuma ko wannen su yana iƙirarin mallakar filin da a ka bada diyyar. Shi ya sa masarauta ta yi maza ta shiga maganar domin samar da zaman lafiya.
"Yanzu mun bari har sai kotu ta ta yi hukunci a kan ƙarar da s ka shigar,"
No comments