Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce za su "tabbatar ba a samu ƙarancin kuɗi ba" a gwamnatinsa wajen samar da tsaro a faɗin ƙasa...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce za su "tabbatar ba a samu ƙarancin kuɗi ba" a gwamnatinsa wajen samar da tsaro a faɗin ƙasar kuma "saura ƙiris a samu nasara a yaƙi da 'yan ta'addan Boko Haram masu fakewa da Musulunci".
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake taya al'ummar Musulmi murnar bikin Ƙaramar Sallah a yau Lahadi, yana mai cewa "muna da dalilin da ya sa za mu yi bikin (Sallah) cikin ƙwarin gwiwa".
"Yaƙin da ake yi da 'yan ta'adda da suke fakewa da Musulunci ya kusa zuwa ƙarshe," in ji shi cikin wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar. "Yaƙin ya ɗauki lokaci kuma da wuya. An kusa cimma nasara."
Buhari ya yaba wa aikin hukumar NDLEA mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa ta ƙwace fiye da kilogiram miliyan 3.4 na miyagun ƙwayoyi da suka kai darajar naira biliyan 130 a 2021, da kuma kama manyan masu safarar ƙwayoyin a farkon 2022.
"Domin ƙarfafa wa hukumar da lamarin ya shafa gwiwa, Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin a ƙara wa jami'an tsaro 3,500 girma, da kawo kayan aiki da kuma ba da horo," a cewar Garba.
"Haka nan Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin haɗa kai da aiki tare tsakanin jami'an tsaro, yana mai cewa an kawo ƙarshen tsarin rashin aiki tare tsakanin hukumomi da kuma tabbatar da cewa ba a samu ƙarancin kuɗi ba wajen samar da tsaro ga 'yan ƙasa."
No comments