Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaban Senegal Ya Bayyana Goyan Bayansa Ga Idrissa Na PSG

  Shugaban Kasar Senegal Macky Sall ya bayyana cikakken goyan bayansa ga ‘dan wasan kungiyar PSG Idrissa Gana Gueye wanda ke shan caccaka a ...

 


Shugaban Kasar Senegal Macky Sall ya bayyana cikakken goyan bayansa ga ‘dan wasan kungiyar PSG Idrissa Gana Gueye wanda ke shan caccaka a Faransa saboda kin sanya rigar dake dauke da launin goyan bayan ‘Yan luwadi da madigo.

A sakon da ya aike ta Twitter, shugaba Sall ya bayyana goyan bayansa ga Idrissa, inda ya bayyana cewar ya dace a mutunta addinin da yake bi.

Kungiyar PSG ta ki sanya Idrissa a karawar da ta yi da Montpellier a karshen mako saboda yaki sanya rigar dake dauke da launukan goyan bayan ‘Yan luwadi da madigo da ake kira LGBTQ.

Mai horar da ‘Yan wasan kungiyar PSG Mauricio Pochettino ya sanar da cewar Idrissa yaki fitowa karawar ce saboda dalilai na kashin kan sa amma ba domin rashin lafiya ba, abin da ya sa wata tashar Rediyo bayyana cewar da gangan yaki fita wasan saboda kar ya saka rigar dake dauke da alamun kamar yadda ya yi a shekarar da ta gabata.

Kasar Senegal na girmama Idrissa tare da abokan wasan sa dake yiwa kasar wasanni, kuma yana daga cikin ‘Yan wasan da suka lashe mata gasar cin kofin Afirka na farko a Masar a watan Fabarairun da ya gabata.

Idrissa na ci gaba da samun sakon goyan baya daga bangarori daban daban ta kafar intanet, kuma daga cikin su harda Ministan wasanni Senegal Matar Ba da Firaminista Mahammed Boun Abdallah Dionne suka aike masa kamar yadda RFI Hausa ta labarto.

No comments