Daga Ammar M. Rajab Rahotanni sun shigowa Jaridar MADOGARA inda aka labarta mana cewa an tsinci wani matashi cikin jini sharkaf a daki...
Daga Ammar M.
Rajab
Rahotanni sun shigowa Jaridar MADOGARA inda aka
labarta mana cewa an tsinci wani matashi cikin jini sharkaf a dakinsa da alamu
na sara da adduna da wuka a jikinsa da kansa.
Matashin mai suna Abdulmalik Isa, ya kasance direban
Babban mota ne dake aiki da wani Kamfani a Kaduna. Sai dai lamarin ya auku ne a
dakinsa dake cikin Jushin Zariya ta jihar Kaduna.
Wani makusancinsa ya labarta mana cewa; “Bayan an yi
kwana biyu cur ba tare da an ganshi a gida ba, a gidan kuma aka dauka ya koma
wurin aikinsa ne, ashe bai je ba, a safiyar jiya Talata ne wurin aikin na shi suka
kira suka ce bai fa dawo aiki ba sam, jin hakan yasa aka bazama neman shi, ko da
aka duba dakin shi sai aka ganshi cikin jini, kanshi da kunnen shi da sara,
jinin ma har ya gaji ya tsaya ne da kanshi, fuskarsa ta kumbura”, ya tabbatar
mana.
Ya ci gaba da cewa; “bayan an kai shi asibitin an yi
masa hoto aka ce ƙashin kokon kansa ya karya, an yi masa dauri an kuna yi masa
dinki duka akan”, ya labarta mana.
Ya karkare da cewa; “sannan an yi masa allurori sai
dai har ya zuwa yanzu bai farfado ba”, ya tabbatar.
Makusanta da abokai sun bayyana matashi Abdulmalik a
matsayin matashi mai kokari wajen neman na kansa, sannan yana da kirki, kuma
mutum ne mai fara’a ga jama’a.
Ya zuwa yanzu ba a tabbatar da yaushe aka yi masa
wannan aika-aikar ba, kuma ko su wane ne suke da alhakin aikata masa hakan.
No comments