Turai Ta Zabtare Yawan Fetur Da Take Karba Daga Rasha


Shugabannin kasashen Turai sun amince su rage kusan kashi 90 cikin 100 na mai da Rasha ke shigarwa cikinsu nan da karshen shekara.

Sai dai wannan ba zai shafi kasar Hungary ba, wadda ta dogara kacokan ga ɗanyan man Rasha.

An cimma wannan ne bayan shafe daren jiya su na tattaunawa a Brussels, wannan kuma shi ne mataki na baya-bayan nan da EU ta dauka tun a martani kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

Shugabar hukumar gudanarwar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta jinjinawa matakin.

Ta ce ta yi matukar farin ciki da amincewar da shugabanin suka yi na kakaba karin takunkumai kan Rasha.

Post a Comment

0 Comments