Wasu al'ummar Musulmi sun gurdanar da Sallar Idi a jihohin Sokoto da Kebbi da ke arewa maso yammacin Nijeriya. A jihar Sokoto, S...
Wasu
al'ummar Musulmi sun gurdanar da Sallar Idi a jihohin Sokoto da Kebbi da ke
arewa maso yammacin Nijeriya.
A
jihar Sokoto, Sheikh Musa Lukwa ne ya jagoranci Idi da mabiyansa a ranar
Lahadi.
Haka
ma a garin Jega na jihar Kebbi sun gudanar da Sallarsu ta Idi.
Sarkin
Musulmi Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar ya ayyana ranar Litinin a matsayin
ranar Sallah bayan kasa ganin watan Shawwal a ranar Asabar.
Samun
irin wannan saɓani ba sabon abu ba ne a Nijeriya, inda a shekarar da ta gabata
ma fitaccen Malamin Taijjaniyya Sheikh ÆŠahiru Bauchi ya gudanar da Idi ba tare
da bin umarnin sarkin Musulmin ba.
No comments