Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Sun Hallaka Janaral Da Wasu Sojoji 7 A Jihar Taraba

Akalla sojoji takwas ne da suka hada da Birgediya Janar, Kwamandan Bataliya ta 93 ta Bataliyar Takum a Jihar Taraba, wanda wasu ...


Akalla sojoji takwas ne da suka hada da Birgediya Janar, Kwamandan Bataliya ta 93 ta Bataliyar Takum a Jihar Taraba, wanda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kashe a ranar Talata.

Shugaban karamar hukumar Takum, Honorabul Shiban Tikari, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Jaridar LEADERSHIP ta wayar tarho lokacin da aka tuntube shi.

Ko da yake Tikari bai iya bayar da cikakken bayanin lamarin ba, ya shaida wa wakilinmu cewa shi da wasu jami’an tsaro na cikin daji suna ci gaba da zakulo gawarwaki da sauran mutanen da suka bata, wadanda ke cikin ayarin motocin Janar na Sojoji a lokacin da aka kai harin.

Wani ganau da yaki bayyana sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce lamarin ya faru ne a tsakanin Takum da kauyen Tanti da ke kan babbar hanyar Takum zuwa Jalingo.

Majiyar ta ce Birgediya Janar na kan hanyarsa ta zuwa Jalingo a ranar Talata lokacin da lamarin ya faru.

Anga Hotunan mutanen da aka kashe a yayin baje kolinsu lokacin da ‘yan bindigar suka sassare jikinsu da adduna.

Ko da yake wasu daga cikin mutanen yankin da suka zanta da wakilinmu sun ce har yanzu GOC ba a ganta ba yayin da wasu suka dage cewa gawarsa na cikin gawarwakin da aka gano kawo yanzu.

“Ba mu so mu yi magana sosai a yanzu da ba mu samu cikakken bayani ba, har yanzu ina cikin daji tare da wasu sojoji, muna ta kokarin ganin an samu duk mutanen da ke cikin ayarin,” In ji Tikari.

A halin da ake ciki kuma, wasu mutane da ake zargin ‘yan fashi ne a ranar Talata da misalin karfe 9 na dare sun jefa bam a cikin ginin wani sansanin soji da ke dauke da gadar 6, Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Ginin sojojin yana daura da Amazon a kan titin majalisar dokokin jihar Taraba.

Wadanda suka zanta da LEADERSHIP a yankin sun ce ‘yan bindigar da suka jefa bam din suna wucewa ne a kan titin da ke daf da katangar yayin da suka jefa abin cikin harabar sansanin sojoji.

Binciken da aka yi a sansanin ya nuna cewa ba a samu asarar rai ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

No comments