Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Sun Sace Jagoran Methodist A Nijeriya

‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane a Najeriya sun sace shugaban mabiyar darikar ‘Methodist’ na Kiristocin kasar Samuel Kanu a Jihar Abia ta...


‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane a Najeriya sun sace shugaban mabiyar darikar ‘Methodist’ na Kiristocin kasar Samuel Kanu a Jihar Abia tare da wasu limaman cocin guda biyu.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar wadda ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce, ta baza jami’anta domin farautar wadanda suka aikata laifin da kuma kubutar da Kanu.

Matsalar tsaro na ci gaba da tabarbarewa a sassan Najeriya, yayin da garkuwa da mutane domin karbar diyya ya zama ruwan dare.

‘Yankin kudu maso gabashin Najeriya na fama da matsalar Yan aware dake fafutukar kafa kasar Biafra, abinda ke sanya su arangama da jami’an tsaro akai akai.

A makwannin da suka gabata, 'yan bindigar da ake kyautata zatin Yan awaren ne sun kashe wani soja da matar sa da suka je gida domin sanar da shirin bikin su, yayin da a makon jiya aka kashe dan majalisar dokokin jihar Anambra.

No comments