Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

‘Yan Boko Haram Sun Yi Wa Farar Hula 40 Yankan Rago A Borno

Mayakan Boko haram sun kashe fara hula 40 a karamar hukumar Kala Balge ta jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya. Rahotanni sun ce dimbi...


Mayakan Boko haram sun kashe fara hula 40 a karamar hukumar Kala Balge ta jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya.

Rahotanni sun ce dimbim ‘yan ta’adda ne suka yi wa farar hula da basu dauke da makami kawanya, inda suka yi ta yi musu yankan rago a ranar Lahadi.

‘Yar majalisar wakilai ta Tarayyar Nijeriya da ke wakiltar mazabar, Zainab Gimba ta tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labari.

 Wata majiya ta tsaro ta shaida wa jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa  Najeriya ta ce an kashe  msu sana’ar gwangwan da dama, kuma tuni aka binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Wani rahoton kuma ya yi nuni da cewa gwamman ‘yan ta’adda ne suka kai wa farar hular, wadanda kananan manoma ne farmaki da takuba.

yanzu ana nan ana laluben sauran gawarwakin wadanda ba a gani ba a cikin dazukan da lamarin ya auku.

No comments