Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

''Yan Kwankwasiyya Na Tsoron PDP Ta Tsayar Da Atiku Abubakar'

Wasu bayanai da Jaridar MADOGARA ta tattara na nuni da cewa abin da yasa Kwankwasawa ke goyon bayan Gwamna Wike na jihar Ribas y...


Wasu bayanai da Jaridar MADOGARA ta tattara na nuni da cewa abin da yasa Kwankwasawa ke goyon bayan Gwamna Wike na jihar Ribas ya yi nasara kan Atiku Abubakar da sauran 'yan takarar dake neman tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a PDP shi ne; a tunaninsu hakan zai bai wa dan takararsu na NNPP, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso damar lashen zaben 2023. Domin a cewarsu APC ta zama matacciyar gwanda, kuma da 'yan Arewa su zabi Nyesom Wike gwara su zabi dan takararsu Kwankwaso na NNPP. 

Kwankwasawa na ganin tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa a PDP barazana ce ga dan takararsu na NNPP. 

Sai dai masana kan harkokin siyasa sun tabbatarwa da Jaridar MADOGARA cewa NNPP na iya tasiri a zaben 2023 musamman a jihohin Kano, da Jigawa, amma babu ta inda za ta iya lashe zaben shugaban kasa na 2023. 

No comments