Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: ASUU Na Shirin Janye Yajin Aiki

Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Ƙasa, ASUU, za ta iya janye yajin aikin da ta ke yi a ko wanne lokaci da ga yanzu, kamar ya...



Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Ƙasa, ASUU, za ta iya janye yajin aikin da ta ke yi a ko wanne lokaci da ga yanzu, kamar yadda jaridar DAILY POST ta jiyo.

Wani mamban kungiyar da ya zanta da wakilin jaridar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce a halin yanzu malaman jami'o'in da ke yajin aikin na tunanin janye yajin aikin na tsawon watanni uku.

A cewarsa, dakatarwar na iya zama na tsawon watanni uku kacal, yana mai cewa za a ci gaba da tattaunawa da Gwamnatin Tarayya a cikin wa’adin watanni ukun.

Ya ƙara da cewa gazawar gwamnati wajen biyan bukatun ASUU ɗin cikin watanni ukun zai haifar da yajin aikin sai-baba-ta-gani.

Hakan na zuwa ne sa’o’i kaÉ—an bayan da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya roÆ™i ASUU da ta duba halin da É—alibai ke ciki, ta janye yajin aikin.

Kungiyar ta fara yajin aikin gargadi ne a ranar 14 ga watan Fabrairu saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatunta da aiwatar da wasu yarjejeniyoyin da bangarorin biyu suka kulla a baya.

A ranar Litinin 9 ga watan Mayu ne aka tsawaita matakin na masana'antar da wasu makwanni 12, wanda ake sa ran zai wuce ranar 9 ga watan Agusta.

No comments