YANZU-YANZU: Ministan Buhari Ya Ajiye Mukaminsa


Labarin dake shigowa Jaridar MADOGARA a halin yanzu shi ne, karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba, ya ajiye mukaminsa na minista jim kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa dukkanin ministocinsa masu neman takara umurnin su ajiye mukamansu nan da kwana 5. 

Shugaba Buhari ya bada umurnin ne a yau Laraba a taron Majalisar zartaswa ta kasa. 

Nwajiuba na daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a Jam'iyyar APC. 

Tuni ya saya fom din tsayawa takarar akan naira miliyan 100.

Post a Comment

0 Comments