YANZU-YANZU: Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Kano, Alhassan Rurum Ya Fice Daga APCTsohon Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum ya fice da ga jam'iyar APC.

Rurum ya sanar da ficewar ta sa ne a wata tattaunawa da manema labarai ta wayar tarho a yau Lahadi, inda ya koka cewa ba a bin ƙa'idojin dimokaraɗiyya a jam'iyar.

Ya ce ya yi iya ƙoƙarin sa na ya ga an tabbatar da bin ƙa'idojin dimokaraɗiyya wajen fitar da ɗan takarar gwamna a jam'iyar amma hakan ya ci tira.

Shi ya sa ya ce ya fice da ga jam'iyar, inda ya kuma nuna cewa tuni ya fara tuntuɓar abokan harkar siyasar sa a kan jam'iyar da zai koma.

Daily Nigerian Hausa ta gano cewa Rurum ya ɗauki wannan mataki ne bayan da a ke ta raɗe-raɗi mai ƙarfi cewa Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya zaɓi mataimakin sa, Nasiru Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamna, shi kuma Murtala Sule Garo, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, ya zama mataimaki a takarar.

Ƙarin bayani na nan tafe...

Post a Comment

0 Comments