Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zan Ba Tsaron Rayuka Da Dukiyoyin Al'umma Muhimmanci Idan Na Zama Gwamnan Katsina, Cewar Dan Takarar Abbas Masanawa

Mai neman jam'iyyar APC a jihar Katsina ta tsayar da shi takarar gwamnan jihar Alhaji Abbas Umar Masanawa, yace muddin Allah...Mai neman jam'iyyar APC a jihar Katsina ta tsayar da shi takarar gwamnan jihar Alhaji Abbas Umar Masanawa, yace muddin Allah Ya bashi damar zama gwamna a jihar zai ba tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma muhimmanci sosai.

A taron manema labarai a Katsina domin sanar da al'ummar jihar Katsina ta hannun 'yan jarida aniyarsa ta neman tsayawa takarar Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Abbas Masanawa yace kusan matsalar da ake fama da ita kenan a Katsina da ma sauran sassan kasar, wato matsalar, da yace zai yi amfani da ilmi da gogewar da ya samu wajen ganin an yo wa tufkar hanci cikin kankanin lokaci.

Ga cikakken jawabin nasa;

A yau wannan rana mai dumbin tarihi da tarin albarka, nake kara godiya ga Allah madaukaki sarki da ya kawo mu wannan lokaci da rai da koshin lafiya. Allah mun gode. Muna masu farincikin yi muku marhabin tare da yin godiya marar iyaka da kuka samu damar halartar wannan gagarumin taron da muka kira. Da fatan Allah Ya sa mana albarka, Amin.

2. Dalilin kiran ku, 'yan jarida, mutane masu muhimmanci a cikin al'umma, shi ne domin ta hannunku, mu sanar da daukacin al'ummar jihar Katsina masu tarin albarka aniyarmu ta neman tsayawa takarar Gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyar APC a babban zabe mai zuwa na shekarar 2023.

3. Bayan mun tuntubi bangarori daban-daban, musamman daga masu ruwa da tsaki na jam'iyya da iyayen kasa (masu rike da sarautun gargajiya da shugabannin addini da dattawan jihar Katsina da masu ruwa da tsaki a harkar ilmi da kungiyoyin kwadago da 'yan jarida (ku din nan, da nake magana daku yanzu) da ma'aikatan gwamnati da kungiyoyin 'yan kasuwa da kungiyoyin mata da matasa da mutane masu bukata ta musamman da kuma dalibai 'yan asalin jihar Katsina a dake karatu a makarantun mu na ciki da wajen jihar nan. 

A wannan gabar ne, nake gabatar da kaina a matsayin wanda ke fatar samun tikitin zama gwamnan jihar Katsina a karkashim jamiyyarmu mai albarka ta APC da nake fatar yi wa jihar aiki tukuru cikin yardar Allah idan na zama gwamnan jihar Katsina a babban zaben shekarar 2023 mai zuwa.

4. Ina mai amfani da wannan dama, domin sanar da ku cewa tuni na sayi takardar cikewa wato 'form' a babbar hedikwatar jam'iyyar APC dake Abuja kuma na cike kamar yadda ake bukata. Sannan tuni har tawagar kasu tantance 'yan takara, ta tantance ni ba tare da samun wata tangarda ba.

5. 'Yan jarida, Ina so ku bani dama, in sanar da al'ummar jihar Katsina ta hannunku cewa, babban abin da ya sa nake so tare da fatar zama Gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyar APC, bai wuce na shimfida shugabanci na adalci a cikin al'umma ba. Mulkin da zai sa farinciki a cikin al'ummar jihar Katsina. 

Mulkin da zai sa al'ummar jihar Katsina su yi tunkaho, su yi rawa gaban hantsi a duk inda suka samu kansu da yardar Allah.  A wannan gaba, mun yi tanadi mai kyau a fannoni daban-daban na dorawa daga nasarorin da  gwamnatin Rt. Hon. Aminu Bello Masari CFR, FNIM ta samu kuma take cikin samu a halin yanzu.

6. Al'ummar jihar Katsina, ba tare da alfahari ba, duba da irin kwarewa da gogewar da na samu a matsayina na kwararren ma'aikacin gwamnati, a haka, na samu damar zama shugaban hukuma mai matukar tasiri da muhimmanci a Nijeriya wato hukumar buga muhimman takardu da a turance ake kira da Nigerian Security Printing and Minting. 

Allah Ya hore min ilmi mai zurfi na boko da na addini, sannan na samu gogewa a aikin gwamnati, kazalika na san manyan mutane da kamfanoni a ciki da wajen Nijeriya da hakan zai taimaka a bunkasa tattalin arziki da walwalar jama'a ta yadda jihar mu ta Katsina za ta samu cigaba mai dorewa cikin hukuncin Allah.

7.  Abokan hudatayyar mu 'yan jarida, ina mai bugun kirjin cewa na shirya tsaf, domin tunkarar irin nauyin da ke kan kujerar Gwamna musamman a jiha irin Katsina da take fama da kalubalen tsaro kamar dai yadda wasu jihohi na Nijeriya ke fuskanta.  Matsalar tsaro, kamar dai yadda kuka sani, ita ce matsala babba da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.  

To a kan haka ne, nake mai tabbatar muku da cewa idan Allah Ya bani dama, na zama gwamnan jihar Katsina, maganar samar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma ne kan gaba a cikin tsare-tsaren da na fito da su domin hana sata da garkuwa da mutane da dakile ayyukan ta'addanci da kawar da sauran ayyukan assha a lungu da sako na jihar Katsina.

8. Kadan daga cikin karin abubuwan da na tsara idan Allah Ya bani dama na zama gwamnan jihar Katsina, na ga cewa sun kara inganta, shi ne ILMI, da ake yi wa kirari da kashin bayan cigaban kowace al'umma, wasu na cewa ILMI, garkuwar dan'Adam domin ganin cewa ya inganta a dukkanin matakai.  

Mai ilmi kamar yadda masu azancin magana ke cewa, ba ya tabewa. Sannan samar da ingantaccen ilmi, hanya ce babba ta kara inganta tsaro a cikin al'umma. Don haka ne na tsara zuba hannun jari mai tsoka a bangaren ilmi idan Allah cikin rahamarsa Ya bani damar zama gwamnan jihar Katsina.

9. Ba zamu gajiya ba, har sai mun ga mun waiwayi sashen kula da aikin gona domin samar da wadataccen abinci da inganta yankunan karkara da samar da tallafin sana'o'in hannu ga mata da matasa,  domin rage radadin talauci da fatara a cikin al'umma da inganta manya da kananan asibitoci domin lafiya ta inganta da ayyukan raya kasa da samar da ayyukan yi da koyarwa tare da horar da sana'o'in hannu da samar da makamashi da kuma inganta sashen ilmin na'ura mai kwakwalwa domin tafiya da zamani.

10. Sannan zamu yi aiki kasa-rika domin al'ummar jihar Katsina su ce gwara da aka zabe mu.  Tsare-tsarenmu gaba daya, ba su wuce na mu kawo zaman lafiya da ci gaban al'ummar jihar Katsina ba. Kazalika, nan ba da jimawa ba, zamu fitar da tsare-tsare yadda lamurranmu na siyasa za su kasance insha Allahu.

11. Daga karshe, ya zama wajibi na yi godiya ga Allah, da Ya bani dama na tsaya gabanku a wannan rana mai dumbin tarihi da albarka domin sanar da ku irin guzurin da na zo wa al'ummar jihar Katsina da shi. Sannan ina matukar godiya gare ku da ku ka samu damar halartar wannan gagarumin taro da muka kira duk kuwa da sanarwar ta same ku cikin kankanin lokaci.

12. Na gode. Allah Ya yi mana jagoranci baki daya.

Wassalam Alaikum.

Abbas Umar Masanawa
Mai neman tikitin takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin Jam'iyyar APC
17/05/2022

No comments