Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Abduljabbar Bai Cancanci Kariyarmu Ba, In Ji Kungiyar Lauyoyi

  Kungiyar lauyoyi masu kare marasa galihu a Nijeriya ta ce Abduljabbar Nasiru Kabara bai cancanci samun kariyarsu ba, irin wadda suke bai w...

 


Kungiyar lauyoyi masu kare marasa galihu a Nijeriya ta ce Abduljabbar Nasiru Kabara bai cancanci samun kariyarsu ba, irin wadda suke bai wa masu karancin gata bayan ficewar lauyansa Ambali Muhammad daga shari'ar da ake yi masa ta yin batanci ga addini.

Wata kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a kofar kudu ce ta nemi a bai wa Abduljabbar kariya daga kungiyar lauyoyin.

Tun daga watan Yunin bara ne yake fuskantar shari'ar yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) wanda gwanati Kano ta ce aikin nasa zai iya tunzura jama'a.

A jiya ne daraktan kungiyar Barista Mukhtar Labaran Usman ya shaida wa wata kotu cewa malamin bai cancanci a ba shi kariya ba saboda yana samun abin da ya wuce naira 30,000 wato mafi karancin albashi da kasa ta yarda da shi.

No comments