Mutumin da ke takarar sanata karkashin inuwar jam'iyyar APC a Yobe ta Arewa a Najeriya, Bashir Sharrif Machina, ya ce ba zai sauka ko ...
Mutumin da ke takarar sanata karkashin inuwar jam'iyyar APC a Yobe ta Arewa a Najeriya, Bashir Sharrif Machina, ya ce ba zai sauka ko ya janyewa kowa takararsa ta majalisar dattawa ba.
Wadannan kalamai na Bashir Machina na zuwa ne a daidai lokacin da take ƙasa take dabo game da makomar siyasar shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ahmed Lawan, bayan ya rasa takarar shugaban ƙasa a APC da ya nema.
Tun bayan kammala zaben fitar da gwani shugaban kasa a APC dambarwa ta kunno kai kan yiwuwar rasa takararsa ta sanata bayan ya shafe fiye da shekara ashirin yana wakiltar al'ummarsa a Majalisun Tarayyar ƙasar.
Rahotanni a baya-bayan nan sun yi ta yaÉ—a cewa Sanata Ahmad Lawan ya samu takarar É—an majalisar da yake kai yanzu, sai dai mutumin da ya ci takarar tun da farko, Bashir Sharif Machina ya ce har yanzu shi ne É—an takarar Sanatan Yobe ta arewa a APC.
Kuma an yi ta samun bayanai da rade-radi da ake ta yadawa cewa wasu jiga-jigan APC na neman tursasawa É—an takarar ya janyewa Ahmed Lawan.
Abin da Machina ke cewa
A tattaunawarsa da BBC, Bashir Machina, ya ce ya fitar da takarda a shafukan sada zumunta wanda ya aikewa jam'iyya, kan tuntubar da aka yi ma sa ko yana nan kan takararsa.
Ya ce shi kuma ya amsa da cewa bai janye ba, kuma yana kan takararsa. Sannan ya ce shi baki da baki Ahmed Lawan bai tuntube shi ba, don haka yana nan kan bakarsa kamar yada jama'a suka zaɓe shi.
Dan takarar ya kuma ce "ko da an tuntube ni ma ba zan janye takarata ba, saboda mutane ne suka zabe ni a zaben fitar da gwani domin na wakilce su.
An kada kuri'a an tantace na yi nasara, don haka duk bayanan da ake yadawa cewa na janye ko zan janye labaran boge ne", in ji É—an takarar.
Bashir ya kuma ce yana kan bakarsa, kuma yana da tabbacin nasara, saboda manufar takararsa ita ce jagoranci nagari, saboda jama'a su samu wakilci na gari.
Akwai "tsare-tsaren da nake son aiwatarwa saboda a shirye nake, na yi kintsawar da zan kasance wakili nagari ga jama'ata".
Ko bangaren Ahmed Lawan sun yi martani?
BBC ta yi ƙoƙarin ji daga ɓangaren Sanata Ahmed Lawan, amma mataimakansa na musamman da muka tuntuɓa, ba su mayar da wani martani ba tukunna.
Amma dai wannan yanayi bai zo da mamaki ba, don ba wannan farau ba da ake samun mutanen da suka fadi a takara suke komawa domin neman makamansu na baya.
Mutanen da suka faɗi zaɓen fitar da gwani irinsu gwamnan Bauchi, Bala Muhammad Kaura, ya koma nema takarsa ta gwama a karo na biyu bayan gaza cimma muradansa na neman takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP.
Mutumin da a farko aka sanar cewa shi ne ya yi nasara a zaben fitar da gwani na PDP ya janyewa Kaura, bayan sake maimaita zaben fitar da gwani a Bauchi.
Hakazalika a Sokoto an ga yadda Gwamna Tambuwal, shi ma ya koma ya nemi tikitin Sanata bayan rasa damar cimma burinsa ta neman kujerar shugaban kasa.
Shi ma Tambuwal ya samu É—an takarar da da fari aka ce shi ya yi nasara, ya jenye masa.
No comments